You are here: HomeAfricaBBC2023 01 30Article 1704815

BBC Hausa of Monday, 30 January 2023

Source: BBC

Yadda matan Afghanistan ke rayuwa cikin tsoro da fargaba

Hoton alama Hoton alama

Matan ƴan Afganistan na ta bayyana abubuwan da ke rayukansu da sakwanni ga BBC, inda suke yin bayani dalla-dalla, yadda kamar da wasa aka tauye musu rayuwarsu da walwalarsu, da `yancinsu – a lokacin da suke cikin tsaka mai wuya na yanayin dari mai tsanani, ga karancin abinci da kuma yawan daukewar wutar lantarki.

Wata 17 da Taliban ta karbe ragamar kasar Afganistan, kuma kasar tana fama da dinbin kalubale.

Rabin al`umar kasar tana fama da matsananciyar yunwa, ga tsananin sanyi, ga matsalar wutar lantarki da kuma durkushewar tattalin arziki.

Rayuwa ta yi wa kusan kowa kamun-kazar-kuku, sannan matan da suke kasar suna ganin an tauye musu `yancinsu- an takaita musu `yancin aiki, da na karatu da na walwalar cudanya, a karkashin dokokin da masu jagorantar kasa da suke da ra`ayin musulunci suka shimfida.

BBC tana ta zantawa da mata da suke sassa daban-daban na kasar, da suke ta aiko da sakonni na muryoyi da kuma a rubuce. Sun bayyana yadda dare guda rayuwarsu ta sauya a karkashin mulkin Taliban.

Saboda dalilai na kariya muna sakaya wasu daga cikin abubuwan da za su sa a iya gane ko su wane ne su.

Gargadi: Wannan labari yana kunshe da bayanai na kunar-bakin-wake.

'Rayuwar yanke ƙauna'

Tun karbar mulkin Taliban abubuwa da dama sun shafi rayuwar mata daga dukkan bangarori na rayuwa, har da wata ma`aikaciyar agaji daga Badakhshan, daya daga yankunan kasar da suke can karkara kuma mafi fatara da talauci.

A farko-farkon watan Disamba, Taliban ta fitar da wani umarni da yake haramta wa mata yi wa kungiyoyi da ba na gwamnati ba (NGOs) aiki.

Sun kare kansu cewa sun ba da umarnin ne saboda wata mata da take aiki da irin wadannan kungiyoyi ta saba wa dokar suturta jiki, ba ta sa hijabi ko gyale ba.

Ana ganin haramcin a matsayin barazana ga ayyukan gaugawa na jinkai da ceton rayuka a kasar, da kuma take hakkokin da mata suke da su.

“Mun sadu da mutane daban-daban;  za mu yi magana da mata, da maza, da yara, da tsofaffi,” in ji ma`aikaciyar agajin wacce a yanzun ba ta iya gudanar da aikinta.

“Mukan musu tambayoyi a game da matsalolinsu da bukatunsu , sannan mu aike wa ofisoshinmu rahoton matsalolin da muryoyinsu.

Ta ce “Ina jin dadi da kuma matukar farin cikin taimaka wa mutanena”

Mutane su a kalla 124 ne suka riga mu gidan gaskiya sakamakon bugawar yanayi na sanyi, kamar yadda Ma`aikatar Tafiyar da Lamura na Bala`o`i ta bayyana, kuma an fi bukatar agaji a yanzun fiye da kowanne lokaci.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce a karshen shekarar da ta gabata, kashi biyu cikin kashi uku na al`umar Afganistan, yana bukatar agaji na jinkai.

Ta ce “Muna raye ne kawai ba tare da wata fata ta ci gaba ba. Ina kallon fina-finai, da bidiyo ta soshiyal midiya da shirye-shirye na talabijin saboda ba ni da abin yi,”

Ma`aikaciyar agajin har ila yau tana sa ran karatun digiri na biyu, sai dai kamar yadda ta fada, wannan mafarki ko buri nata, ya “rushe”

“Yanzun na gaji da zaman kashe wando. In yini ba wani aikin da na yi. Ba ma zan iya fita waje a tsanake ko hankalin kwance ba.”

Ta ce ta sha bakar wuya a hannun Taliban.

“Da na fita, sai su tsayar da ni a wuraren binciken ababen hawa su ce in sa hijabi, da rufe fuskata da gashin kaina. Duk da ina sanye da hijabin da ya dace, sai sun dakatar da kai, su ba ka umarnin ka gyara hijabin”

`Ba abin da na iya yi`

Wata maidinka tufafi a Afganistan ta yi suna wajen dinke-dinke na gargajiya da na zamani. Matar wacce take cikin shekarunta 30 da haihuwa, ita kadai ce take kula da gida, da tallafa wa mijinta da `ya`yansu kafin Taliban ta umarce ta, ta rufe sana`arta.

“Ba ni da wani abin yi idan na tashi da safe; in yi sallah, in shirya abin karin kumallo da sharer gida,” in ji ta.

“A da, ina dinka kaya iri daban-daban ciki har da kayan sawa na amare, da na yara, da dinki na gargajiya. Ina sa kananan madubi da sauran abubuwa na kyale-kyale a jikin tufafi in dinke su”

Tuni ta dauke shagon nata daga kasuwa ta kai shi wani kauye, duk da haka sai da Taliban ta bi ta, ta tilasta mata rufe shagon.

“An rufe mun shagona;  ba a barin mata su yi aiki. Masu kawo mun dinki suna ta tambayata me ya sa na rufe shagona, kuma ina shaida musu cewa b azan iya bude shagon ba, amma zan iya musu dinki a gidana.

“Ba zan iya kasancewa da ilahirin shagona a gidanmu ba, saboda gidanmu karami ne, kuma karamin keken-dinki kawai nake da shi da nake iya dinkin da shi a gida.

“A yanzun `yan kananan dinke-dinke masu sauki nake iya yi, ba dinkunan bukukuwa ko na walima, saboda ba ni da na`urorin.” Kamar yadda ta shaida wa BBC.

“A yanzun haka ni da mijina ba mu da aikin yi, kuma a kullum, matsalarmu ta rashin kudi sai karuwa take yi. Kuma `ya`yanmu mata ba sa iya tallafa mana;  wasu lokutan `yan uwa da dangi ne suke taimaka mana, batun ke nan”

'Dafin Da Ke Kisa Sannu A Hankali'

Taliban na karbar mulki, ilimin mata ta fi karkata gare shi. Gwamnatin ta hana `yan mata zuwa makarantun sakandare a Satumba na 2021, sannan da ta dawo a watan Maris na shekarar da ta gabata, ta juya. Har ila yau an hana mata halartar jami`o`i a watan Disamba.

Wata mai nazarin hankalin mutane da take aiki a matsayin malamar makaranta a wata makaranta ta sirri, inda take koyar da aji da ke makare da `yan makaranta 70 da suke son yin karatu- wanda ya fi karancin shekaru, shekarasa 10, wanda ya fi shekaru kuma, shekararsa ta haihuwa 20.

Tana kuma zaman gwajin hankalinsu da na iyayensu.

“Kafin haramcin, a daidai wannan lokaci ina ofis, ko a makaranta. Ba dadi yadda komai ya koma, daga abubuwan da muka saba yi kullum zuwa yadda muke tafiyar da rayuwa a yanzun,”  ta bayyana a cikin sakon muryarta da ta aiko wa BBC.

Ta ce tana samun sako fiye da 30 a dare daga `yan mata da suke so su shiga ajinta- ta ce a kullum yawan sai karuwa yake yi.

“Yara ne `yan mata da suke cikin yanayi da ya fi nawa tabarbarewa da muni, kuma suna cike da tunani na kashe kansu. Suna so su kashe kansu da kawo karshen rayuwarsu, saboda sun rasa kowanne abu da suke da shi a da, da kuma mihimman bukatunsu na rayuwa. “

Ga ita mai ilimin karantar hankalin mutanen, abu mafi firgitarwa da ban tsoro da macen da take Afganistan ba ta fatan ta gamu da shi, shi ne Taliban ta tsayar da ke a wuraren binciken ababen hawa.

Ta ce “Kikan ji kamar numfashinki zai dauke,”

“Watakila ba za su tambaye mu, mu ba su lambobin wayarmu ko bincikar jakunkunanmu ba. Ba a wadannan abubuwa amma suna mana kisan mummuke, wato suna kashe mu sannu a hankali- kamar dafin da yake kisa a hankali.”

“Suna firgita mu, suna sawa muna jin.. Ina nufin ... haifar da batun cewa ba za su kashe mu da harsashi ba, amma za su kashe mu da firgici. Don idan suka tambayeki ina muharraminki kuma fa?

Idan suka tambaye ki ina kike yi wa aiki?”

'Na fi samun walwala'

Omaro-Tah malama ce a wata madrassa (makarantar addini) kuma daliba da take shekarar farko ta karatu a makarantar koyon aikin likita.

Ba kamar sauran matan da muka ji daga gare su ba, ta ce ta fi walwala a karkashin Taliban.

“Muna matukar farin ciki a game da tsaro. Ya fi inganta yanzun. Muna murna da raba wuraren karatu.

(Mata) suna walwala, kuma za su fi iya yin karatu fiye da a can baya. Har ila yau yana cikin addininmu cewa a raba wuraren karatu na mata daban, na maza daban,” kamar yadda ta bayyana.

Wakazalika Omaro-Tah tana goyon bayan dokokin da aka sa a game da tufafin mata.

Tun watan Mayu na shekarar da ta gabata, aka umarci mata su hijabi da rufe fuskokinsu a lokacin da suke bainar jama`a.

“Kamar yadda addininmu yake bayani, muna bukatar mu rufe jikinmu. Ya fi dacewa ga (mata), kamar yadda ta shaida wa BBC.

Sai dai ta ce akwai wasu koma baya da suka auku sakamakon karbar mulki da Taliban ta yi, da suka hada da “koma-baya a matsayin tattalin arzikin jama`a, da rashin aikin yi, da rufe masana`antu da hijirar da mutanenmu suke yi zuwa sauran kasashen saboda rashin aikin yi.

“Wadannan batutuwa sun shafi dabi`un mutane. Sai dai ina cike da fatan za a magance dukkan wadannan batutuwa,”